Fassarar Aminu Bala Madobi-Daga Kano
Hukumar bunkasa kananu da matsakaitan masana’antu ta kasa (SMEDAN) ta ce tana shirin kafa cibiyoyin yad’a bayanan kasuwanci a daukacin kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Babban Daraktan Hukumar Mista Olawale Fasanya, ya bayyana haka a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da manufofin kanana da matsakaitan masana’antu a birnin Jos na Jihar Filato a ranar Alhamis.
A cewar Daraktan Hukumar, Shirin zai baiwa masu karamin karfi damar kasuwanci musamman mazauna karkara damar samun bayanai game da shirye-shiryen.
Rahotannin sun ce Bankin Fidelity ya ce matakin zai kara kaimi ga hukumar tare da samar da ci gaba a kafatanin yankunan karkara.
“Muna da shirye-shirye masu tarin yawa Kuma mutane za su samu makudan kudade, matsalar ita ce rashin samun bayanan da suka dace.
“Don haka, wani bangare na dabarun da muke son amfani da shi don magance wannan matsala ita ce samar da cibiyoyin bayanan kasuwanci a duk fadin kananan hukumomin.
“Ba za mu iya kasancewa a ko’ina ba, amma za mu yi aiki tare da jihohi da kuma kananan hukumomi don ganin yadda za mu kara zurfafa bayanan mu cikin kasa” in ji shi
Rahotannin sun kara dacewa ko da a tattaunawar baya bayannan da masu ruwa da tsaki suka gudanar, Fasanya ya ce an yi ta ne domin samun ra’ayoyi da shawarwari daga masu ruwa da tsaki a matakin jiha akokarin inganta ayyukan hukumar.