Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya CONUA ta ce mambobinta ba sa cikin yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya take gundanarwa a fadin kasa.
A cewar wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Niyi Sunmonu, ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Talata, kungiyar ta ce ba ta cikin yajin aikin domin kungiyoyin NLC da TUC basu tuntube ta ba kafin tsunduma yajin aikin.