Shugaba Tinubu Yayi Umara

Tinubu Performs Lesser Hajj 750x430.jpeg
Tinubu Performs Lesser Hajj 750x430.jpeg

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya yi aikin Umrah a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Tinubu ya yi amfani da wannan damar wajen yin addu’a ga Allah ya yi masa jagora.

Shugaban ya fara gudanar da ibadar addinin muslunci ne a karshen aikinsa a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya, inda ya halarci taron kolin Saudiyya da kasashen Afirka a ranar Juma’a.

Babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana manufar shugaba Tinubu zuwa kasa mai tsarki domin aikin Umrah a ranar Lahadi da yamma.

Ya bayyana cewa, a cikin wannan tafiya ta ibada, shugaban ya yi addu’o’in samun ci gaba a Nijeriya tare da neman tsarin Allah domin ya jagoranci kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here