Rundunar ‘yan sanda a Legas ta ce ta kama kimanin mutum 400 da take zargi da aikata ayyukan bata-gari a sassan birnin, a watan Janairu.
Mai magana da yawun rundunar ne SP Benjamin Hundeyin ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ce sassan ‘yan sanda 25 ne suka aiwatar da aikin.
Karanta wannan: Kungiyar masu gidan burodi za su soma yajin aikin gama gari
Hyundeyin ya ce ya zama dole su kaddamar da babban samame bisa la’akari da irin korafe-korafen da jama’a ke kai musu da kuma bayanan tsaro da suka tattara.
Ya kara da cewa za’a ci gaba da aiwatar da irin wannan tsarin domin tabbatar da an kakkabe baragurbi daga birnin na Legas.