Ƙungiyar ƙwadago ta NLC za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani

NLC rivers
NLC rivers

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce za ta fara yajin aiki na gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan nan na Yuni.

Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau a Abuja.

Kwamared Ajaero ya ce gwamnati musamman ma kamfanin mai na kasa NNPC na da wa’adin daga yanzu zuwa ranar Laraba ta mako mai zuwa ya mayar da farashin man kamar yadda yake a da idan ba haka ba za su shiga yajin aikin na sai-abin-da-hali-ya-yi da kuma zanga-zanga a fadin Najeriya.

Daman a yau ne shugabannin suka kira wannan taro domin tattaunawa da bayyana matakin da za su dauka bayan da sabon shugaban kasa ya furta cewa zai janye tallafin mai.

Wannan sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan Najeriya, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here