Tinubu ya jajanta wa Indiya kan hatsarin jiragen ƙasa

Bola Ahmed Tinubu sabo
Bola Ahmed Tinubu sabo

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon jaje ga gwamnati da al’ummar Indiya kan hatsarin jiragen ƙasa da ya kashe fiye da mutum 280 a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, Tinubu ya bayyana hatsarin da cewa abu ne mai sosa zuciya.

Sanarwar ta ce ”Ina jajanta wa iyalan mutanen da hatsarin jirgin ƙasa ya rutsa da su a jihar Odisha, muna taya su jimami kan halin da suke ciki.

”Ina miƙa sakon jaje da ta’aziyya ga mai girma firaminista Narendra Modi, da mutanen Indiya tare da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su”, in ji shugaban na Najeriya.

Hatsarin ya rutsa da jiragen ƙasa guda biyu maƙare da fasinjoji da kayayyaki a birnin Baladsore a jihar Odisha da ke gabashin ƙasar.

Fiye da mutum 900 ne suka jikkata a hatsarin wanda ya kasance ɗaya daga cikin hatsari mafiya muni a tarihin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here