Kungiyar Arewa Development Support Initiative (ADSI) ta baiwa zawarawa 50 marasa galihu a jihar Kano tallafin naira dubu hamsin kowannensu domin bunkasa sana’arsu.
Da yake jawabi a wajen taron a ranar Lahadin da ta gabata, Shugaban kungiyar Farfesa Aliyu Abdu ya bayyana cewa wadanda aka zaba zawarawa ne masu kananan sana’o’i da ke bukatar tallafi.
Ya kara da cewa ADSI kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa domin mahawara da kuma kawo dabaru da tallafi da zai kawo cigaba a Arewa. Ta hanyar yan kungiyar na bayar da gudunmawar akalla naira 2,000 duk wata domin yin tallafawa marasa karfi da kuma sauran ayyukan jin kai a Arewa.
‘Kungiyar tana horar da mutane sana’o’in hannu domin inganta rayuwar talakawa da magance wasu matsalolin da yankin Arewa ke fuskanta.
Farfesa Abdu ya ci gaba da cewa kungiyar ta bayar da tallafi sosai ga marasa galihu da suka hada da tallafin kayan aiki na naira miliyan 2.5 ga gidan ajiya na yara dake Goron Dutse a bara.
Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da tallafin yadda ya kamata domin bunkasa sana’o’insu.
Ya kuma godewa shugabannin kungiyar na kasa kan yadda suke ba su goyon baya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Zara’u Nasarasu daga Sallari Babban Giji ta nuna jin dadin ta ga kungiyar tare da yin addu’o’in samun tallafin Allah ga ‘ya’yan kungiyar da iyalansu.
Ita ma Halima Abdullahi daga Sabowar Gandu ta godewa kungiyar tare da yin alkawarin yin amfani da tallafin wajen fadada kasuwancinta da tallafawa marayun ta.