Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), reshen Jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadarin mota da ya auku a hanyar Kaduna Western Bypass.
Kwamandan Sashin, Andre Longkam, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Kaduna.
Ya ce hadarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na rana a mahadar Asibitin Kula da Ido na Tarayya, ya kuma ritsa da wata babbar mota kirar DAF, da wata mota kirar Honda da kuma babur.
Longkam ya ce binciken farko ya nuna cewa motar Honda ta buge babur din, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matukin babur din da fasinja.
“Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a hatsarin,” in ji shi.
Ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, wasu matasa da suka fusata sun banka wa motocin da lamarin ya shafa wuta, lamarin da ya haifar da karin barna.
Kwamandan ya ce jami’an hukumar, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, sun garzaya wurin da lamarin ya faru don shawo kan cunkoson ababen hawa da dawo da zaman lafiya.
A cewarsa, an dauki matakan da suka dace don tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin walwala da hana faruwar wani abu makamancin haka.
Longkam ya nuna damuwa kan hatsarin kuma ya yi kira ga masu motoci da su yi taka-tsantsan, musamman a hanyoyin da ake gyara.
Ya kuma shawarci direbobi da su bi dokokin hanya kuma su guji ayyukan da za su iya kara ta’azzara yanayin gaggawa.
Shugaban na FRSC ya ce bincike kan musabbabin hatsarin na ci gaba da gudana, ya kuma kara da cewa hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a hanyoyin kasar nan. (NAN)











































