Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutun Dimokuradiyya 

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar dimokuraɗiyya.

Jaridar The Nation tace babbar sakatariyar ministirin cikin gida Dr Oluwatoyin Akinlade, ita ce ta bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Babbar sakatariyar ta taya ƴan Najeriyaa murnar zagayowar wannan rana mai cike da ɗumbin tarihi.

Akinlade, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa dimokuraɗiyya a Najeriya ta ga faɗi tashi tun bayan ƙafuwarta. A cikin sanarwar Akinlade ta bayyana cewa duk da faɗi tashin da aka samu a wajen kafuwar dimokuraɗiyya a ƙasar nan, har yanzu ƴan Najeriya basu sare guiwa ba wajen ganin tabbatuwarta.

“Duk da haka ƙasar, hukumominta da abu mafi muhimmanci al’ummar Najeriya sun tsaya kai da fata wajen ganin kafuwar mulkin dimokuraɗiyya.” A cewarta.

“A wannan lokacin mai cike ɗumbin tarihi, ana kira ga ƴan Najeriya da ƙawayen ƙasar da su yaba da ci gaban da aka samu, su yi murna kan nasarorin da aka samu sannan su yi fatan samun dimokuraɗiyya mai kyau a ƙasar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here