A karon farko Fubara ya fara fitowa cikin jama’a bayan dakatar da shi

Suspended Rivers State Governor Siminalayi Fubara attends the Salvation Ministries in GRA Port Harcourt on March 23 202

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana a karon farko tun bayan ayyana dokar ta baci a jihar da kuma dakatar da shi daga aiki.

An ga gwamnan ya isa wurin ibada a hedikwatar Salvation Ministries da ke GRA, Fatakwal, ranar Lahadi.

Fitowar Fubara na zuwa ne kwanaki bayan da shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers a ranar Talata, saboda tabarbarewar siyasa da matsalar tsaro. Sanarwar ta kai ga dakatar da Fubara da mataimakinsa Farfesa Ngozi Odu da kuma daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas.

GmuBrLHXEAA7xxk

A madadin su, shugaban kasar ya nada Ibok-Ete Ibas a matsayin shugaban jihar shi kadai da zai kula da al’amuran jihar na tsawon watanni shida.

Yayin da matakin ya janyo cece-ku-ce daga masu ruwa da tsaki na siyasa da masana shari’a da kungiyoyin farar hula.

GmuBrEybgAAO xX

Sabon shugaban da aka nada shi kadai bai bata lokaci ba wajen karbar mukamin.

Tun bayan da ya hau karagar mulki, ya yi wasu tsare-tsare da suka hada da gudanar da taron gaggawa na tsaro da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi inda ya tabbatar da fitar da kudaden da aka hana, sannan ya ba da umarnin a gaggauta biyan ma’aikatan kananan hukumomin.

Ya kuma kai ziyarar duba aikin sake gina harabar majalisar dokokin jihar, inda ya yi alkawarin tabbatar da kammala shi a kan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya a harkokin mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here