Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Taraba Usman ya rasu

Taraba PPRO Abdullahi Usman 485x430 (1)

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman ya rasu bayan doguwar jinya.

Usman wanda ya kasance kakakin rundunar na tsawon shekaru uku da suka gabata ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a gidansa da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Babban jami’in PPRO na biyu, Gambo Kwache wanda shi ne mukaddashin kakakin rundunar a yayin da Usman ya tafi jinya ya tabbatar da rasuwar PPRO.

Haka kuma, babban aminin marigayi Usman, Ahmed Manga ya tabbatar da rasuwar PPRO.

Manga wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce Usman ya rasu ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi.

Manga ya ce za a yi jana’izar Usman ranar Lahadi da yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here