Tinubu ya yi Allah wadai da samun ayyukan son kai da son zuciya a aikin gwamnati

Tinubu Tinubu drugs 680x430

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da yawaitar son kai, da son zuciya a tsarin bada gurbin aiki ga ’yan uwa a cikin gwamnatin Najeriya, yana mai kira da a ƙarfafa gyaran aikin gwamnati da tsaurara ladabtarwa domin mayar da amincewar jama’a ga gwamnati.

A yayin taron kyautata ayyukan jama’a karo na uku da aka gudanar a cibiyar taro ta fadar gwamnati a Abuja da yammacin Lahadi, shugaban ya yi gargadi cewa raunin hukunci da rashin sa ido cikin tsanaki kan ma’aikata na haifar da rashin imani ga gwamnati tare da rage yadda ’yan ƙasa ke yarda da hukumomi.

Shugaban, wanda ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya wakilta, ya bayyana cewa gazawa wajen aiwatar da doka da rashin ƙarfi a tsare-tsaren kula da ma’aikatan gwamnati na haifar da mummunan kallo ga al’umma, inda ya jaddada bukatar shugabanni su rungumi gaskiya, amanar aiki, aiki da niyya mai kyau da inganci wajen warware matsalolin jama’a.

Shugaba Tinubu ya nanata cewa lokaci ya yi da za a tantance abin da kowane jami’i ya gudanar, yayin da ya nuna cewa lambar yabo ta bana wadda kamfanin kafofin yaɗa labarai mai dabarun ƙwarai tare da ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya ta dogara ne kacokan kan cancanta ba siyasa ba, yana mai yabawa jami’ai hamsin da aka zaɓa daga matakan gwamnatin tarayya da jihohi bisa bajinta.

Ya bayyana cewa duk da cewa cin hanci matsala ce ta duniya, munanan dabi’u irin su son kai, son zuciya da nuna banbanci na gurbata aikin gwamnati da karkatar da hukumomi daga aikinsu na asali, don haka akwai bukatar sa ido mai zaman kansa da hukunci mai ƙarfi ga masu karya doka domin shawo kan wannan matsala.

Karanta: Yunkurin juyin mulki: Yadda Tinubu ya taimaka wajen kare Dimokuraɗiyyar ƙasar Benin – fadar shugaban ƙasa

Ya kuma yaba wa mai shirya taron, Mariam Mohammed, domin ƙoƙarin da ya ce zai sa jami’ai su ƙara dagewa ganin an saka musu ido.

Sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume ya bukaci wadanda suka samu lambar yabo su ci gaba da taka rawa wajen gina ƙasa, yana mai cewa ci gaban aikin gwamnati da al’umma dole ne ya kasance buri na kowa.

Ya yaba wa kamfanin watsa labarai na TBS bisa tsantsar tantancewa, tare da tabbatar da haɗin kan gwamnati wajen inganta ayyukan da ke ƙarfafa gaskiya, tabbatar da adalci da ingantacciyar aiki.

A bana an karrama mutane da kungiyoyi arba’in da hudu bisa sahihan bayanan da suka tabbatar da bajinta, ciki har da gwamnonin Adamawa Ahmadu Fintiri, Bauchi Bala Mohammed, Yobe Mai Mala Buni, Kogi Usman Ododo, da Akwa Ibom Umo Eno, tare da ministoci da shugabannin hukumomi da suka haɗa da Wale Edun, Festus Keyamo, Kemi Nandap, Hafsat Bakari, Zubaida Umar, Olayemi Cardoso, Shehu Mohammed, Imaan Sulaiman-Ibrahim, Buba Marwa (ritaya), da Mohammed Idris, inda aka lura da kirkire-kirkire, jagoranci mai ma’ana da tasiri a hukumomin gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here