Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwa cewa gwamnatin tarayya ta gaza wajen iya shawo kan matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta mamaye da nauyin matsalar tsaro, abin da ya bayyana a matsayin amincewa kai tsaye ga jihohi su kirkiro kuma su tura ƙungiyoyin sa-kai ba tare da zurfin horo ba, haka kuma su ba da dama ga wasu mutane su kafa ƙananan rundunonin tsaro na kansu.
Tsohon gwamnan Kano Kwankwaso, ya ce wannan lamari na iya haifar da barazana ga zaman lafiya mai rauni da ake da shi, domin yana ƙara dagula tsarin tsaro da haɗin kan ƙasa.
Kwankwaso ya ce halin da ake ciki ya nuna cewa gwamnati tana kasa daƙile yaduwar makamai ƙanana da manyan bindigogi, inda ya bayyana cewa bari. jihohi su kafa ƙananan ƙungiyoyin tsaro ba tare da horo ba ya bunƙasa wannan matsala, kamar yadda wasu mutane da suke da muradin siyasa ke amfani da damar wajen kafa rundunonin kansu.
Karanta: Tinubu ya yi Allah wadai da samun ayyukan son kai da son zuciya a aikin gwamnati
Ya kuma nuna damuwa kan abin da ya kira hauhawar nuna bambancin kabila da yanki, yana mai cewa an samu rahotannin da ke nuna yadda ‘yan ƙasa musamman daga wasu sassa na ƙasar ke fuskantar tsangwama, kamawa ba bisa ka’ida ba da kuma azabtarwa a wasu yankuna.
Kwankwaso ya danganta wannan da karin cin zarafi, tsoratarwa da kazafi da ake yadawa a dandalin internet, wanda ake cusa shi da batutuwan kabilanci da addini, yana mai gargadin cewa hakan na barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin dakile wannan yanayi kafin ya fita daga ikonta, yana mai cewa yadda makamai ke ratsa sassa daban-daban cikin sauki abin tsoro ne kuma ba za a yarda da shi ba.
Ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nadinsa a matsayin ministan tsaro, yana mai nuna kwarin gwiwa cewa idan an samu cikakken ƙuduri daga gwamnati, sabon ministan na da kwarewar aiki da za su taimaka wajen dawo da tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar.













































