Zaben 2027: Gwamna Yusuf ya bukaci lauyoyi da su kiyaye bin doka da oda

Abba Kabir Yusuf 680x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga lauyoyi da su kiyaye bin doka da oda tare da bada goyon bayan wajen gudanar da zabe na lumana, gaskiya, mai kuma cike da adalci gabanin babban zaben 2027.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamna Yusuf ya yi wannan kiran ne yayin da ya kaddamar da Taron Shekara-shekara karo na biyu na Kungiyar Matasan Lauyoyin Arewa da aka gudanar a Kano.

Yusuf ya jaddada cewa lauyoyi suna da muhimmiyar rawar takawa wajen kare mutuncin tsarin shari’a, musamman a lokacin shari’o’in da suka shafi kafin zabe da kuma bayan zabe, domin tabbatar da cewa an yi adalci tare da karfafa dimokuradiyya.

Gwamnan ya bayyana matasan lauyoyi a matsayin ginshikin da zai tseratar da dimokuradiyya, kare hakkin ‘yan kasa da kuma bin doka, yana mai cewa su ne a tsakanin kalubalen da bangaren shari’a ke fuskanta a yanzu da kuma makomar wannan aikin lauyanci.

Gwamna Yusuf ya bayyana irin tallafin da gwamnatinsa ta bai wa fannin shari’a, ciki har daukan matasan lauyoyi sama da 70 a Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, rabon kwamfutoci sama da 100 ga matasan lauyoyi, biyan alawus-alawus na kayan ofis da na rigar kotu cda kuma gudanar da shirye-shiryen karfafawa da ci gaba da horar da jami’an shari’a.

Ya kara da cewa gwamnati ta kuma karfafa samar da adalci ta hanyar sauye-sauyen cibiyoyi da kuma inganta hanyar warware sabani ta wasu hanyoyi da ba na kotu ba.

Gwamnan ya yaba wa shugabancin Kungiyar Matasan Lauyoyin Arewa, karkashin Umar A. Chiroma, bisa shirya wannan taron, inda bayyana kwarin gwiwa cewa zai haifar da tattaunawa mai amfani kuma zai ba da gudummawa wajen cigaban fannin shari’a a fadin Arewacin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here