Kungiyar Muslim Rights Concern (MURIC), ta kalubalanci kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) dangane da matsayinta kan nadin ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Farfesa.
Solacebase ta ruwaito cewa ASUU a ranar Litinin din da ta gabata ta bayyana nadin Farfesa Pantami a matsayin ‘wanda aka yi ba bisa ka’ida ba’, inda MURIC ta ce ASUU ba ta koyi darasi ba.
Kungiyar kare hakkin bil adama wadda ke maida hankali kan abubuwan da suka shafi addinin musulunci ta yi magana ta bakin daraktan ta Farfesa Ishaq Akintola a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce, “Kungiyar malaman jami’o’i a jiya ta bayyana nadin Farfesa Pantami a matsayin wanda ya sabawa doka. Gaskiya wannan abun kunya he ga ASUU, domin bata da wani matsayi da za ta bayyana nadin da wata jami’a ta yi ba bisa ka’ida ba tare da amincewar kwamitin nade-nade da kara girma da majalisar jami’ar ta amince da shi.
“Me ASUU ta kasa ke kokarin yi? Menene ainihin matsalarsu? ASUU ta kasa ba ta da hurumin kwace ikon Jami’ar A & P ko ta majalisar ta. A kan wane tushe ASUU ke aiki a matsayin A & P na kasa (idan akwai wani abu makamancin haka) da kuma babbar majalisar jami’o’i?
“Ya kamata ASUU ta kasa ta san iyakarta. Har ila yau, ko akwai wani sashe na tsarin mulkin ASUU da ya ba ta ikon yin watsi da nadin da jami’o’i ke yi? Wannan cin zarafi ne. Babu ƙari, ba kaɗan ba, ”in ji sanarwar.












































