A yau Laraba ne mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai tafi kasashen Gambia da Senegal domin ziyarar aiki ta mako guda bisa gayyatar majalisar dattawan kasar Gambia.
Wata sanarwa da fadar sarkin ta fitar ta ce Sarkin zai fara zuwa Gambiya domin halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai na kasar da za’a yi a ranar Juma’a a matsayin babban bako na musamman.
A cewar sanarwar, zai kuma gudanar da taro da ‘yan kasuwar Gambiya.
Solacebase ta ruwaito cewa Sarkin zai kuma halarci Sallar Juma’a tare da Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow daga bisani kuma ya kai masa ziyarar ban girma.
Sanarwar ta ce ” Ziyarar zuwa Gambiya za ta kare ne da gagarumin liyafar da majalisar dattawan Gambia za ta karrama shi.
“Sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda zai samu rakiyar Ambasada Ahmed Umar, Dan Malikin Kano, Isa Sanusi, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano, Alhaji Dalhatu Abubakar da wasu jami’an kungiyar guda biyu, za su wuce Dakar, Babban birnin kasar Senegal inda kuma ake sa ran zai kai ziyara ga shugaban kasar Senegal Mr. Macky Sall.













































