Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya karɓi mambobin wani kwamitin jagoranci da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa domin samar da tsarin kafa ‘yan sandan jiha, inda ya tabbatar da cewa za a magance damuwar ‘yan Najeriya.
Babban sufeton ‘yan sanda, Olatunji Disu, ne ya kafa kwamitin, inda a ranar 4 ga Maris, 2026 ya ƙaddamar da kwamitin mutum takwas domin su tsara hanyoyin aiwatar da tsarin ‘yan sandan jiha.
A cikin wata sanarwa da mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Malam Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa Jibrin, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999, ya karɓi tawagar karkashin jagorancin shugabanta, Olu Ogunsakin, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a Abuja a ranar Talata.
Ogunsakin ya yi bayani ga mataimakin shugaban majalisar dattawa kan aikin da aka ɗora wa kwamitin tare da neman jagoranci da gudunmawar majalisar dattawa domin inganta rahotonsu.
A nasa jawabin, Barau Jibrin ya yaba wa babban sufeton ‘yan sanda bisa daidaita aikin da shirin sabunta fata na Bola Ahmed Tinubu, wanda ke nufin inganta tsaron ƙasa.
Ya buƙaci kwamitin da ya bai wa batun ɗaukar alhaki da kariya daga amfani da iko ba daidai ba muhimmanci, tare da wayar da kan jama’a.
Ya kuma nuna cewa a yayin sauraron ra’ayoyin jama’a da majalisar dattawa ta gudanar kan gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ‘yan Najeriya sun bayyana damuwa da fargaba kan kafa ‘yan sandan jiha, don haka akwai bukatar samar da tsarin da zai kwantar da hankalinsu.
Ɗaya daga cikin kudurorin da ke gaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulki na neman gyara kundin tsarin mulkin 1999 domin ba da damar kafa ‘yan sandan jiha da na al’umma, da nufin ƙarfafa tsaron cikin gida da kuma zurfafa hulɗa tsakanin jami’an tsaro da al’umma ta hanyar tsarin doka.
Domin tabbatar da haɗa kai, kwamitin majalisar dattawa karkashin jagorancin Jibrin ya riga ya gudanar da tarukan sauraron ra’ayoyin jama’a a shiyyoyi shida na ƙasar, inda aka bai wa masu ruwa da tsaki damar bayar da gudunmawa a kan gyaran kundin tsarin mulki.













































