Masu zanga-zanga sun rufe hanyoyi a Minna

masu zanga-zanga, rufe, hanyoyi, minna
Mazauna Minna babban birnin jihar Neja a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar nan tare da toshe manyan tituna a ciki...

Mazauna Minna babban birnin jihar Neja a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar nan tare da toshe manyan tituna a cikin birnin.

An ji masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa na rera wakokin zanga-zangar, a yayin da jami’an ‘yan sanda ke cigaba da lura da shige da ficen al’umma don samar da tsaro yadda ya kamata.

Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi na kame lamarin ne ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Karanta wannan: Masu kiwon kaji sun koka da asarar Naira Tiriliyan 3 kan tabarbarewar Tattalin Arziki

Mataimakin gwamnan jihar Neja Yakubu Garba a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, ya ce gwamnati na sane da kuncin rayuwa da iyalai ke fuskanta a wannan lokaci.

Kokarin da ‘yan sandan suka yi na shawo kan jama’a kusan ya haifar da tashin hankali yayin da masu zanga-zangar suka nemi ‘yan sandan da su fice, lamarin da ya tilastawa ‘yan sandan harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here