Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da shugaban kasar Amurka Joe Biden a fadar White House.
A Ranar laraba ne shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Amurka Joe Biden a birnin Washington DC.
Hotunan da fadar shugaban kasa ta fitar sun nuna Buhari a ganawarsa da Biden da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a fadar White House a gefen taron shugabannin Amurka da Afirka.
Wnnan na daga cikin jerin tararraki da shugabannin Amurka da kasashen Afirka ke gudanarea a watan Disamba, 2022.












































