Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce akalla mutane bakwai ne aka sanar da bacewarsu a kananan hukumomin Magma da Mashegu (LGAs), sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a ranar Juma’a.
Babban daraktan hukumar Alhaji Abdullahi Baba-Arah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna.
Baba-Arah ya ce sama da gidaje 89 da daruruwan filayen noma ne bala’in ya lalata.
Ya kuma ce, ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da motoci uku, wanda ya biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi da sanyin safiya da aka shafe sa’o’i da dama.