Daga Aminu Abubakar
Wani bincike na SolaceBase ya nuna cewa jihohin Arewa goma sha biyar sun biya Naira miliyan 362.85 a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane tsakanin Yuli 2023 da Yuli 2024.
Baya nin da aka samu a shafin yanar gizo na SBM Intelligence is an Africa-focused market/security intel-gathering consulting firm a cikin rahotonsa na baya-bayan nan mai suna, ‘Economics of Nigeria’s Kidnap Industry’ da aka fitar a ranar Alhamis, ya ce daga cikin adadin Naira biliyan 10.9 da aka nema a matsayin kudin fansa, an samu N1.048bn.
Wannan bitun ya nuna cewa an biya mafi girman kudin fansa a babban birnin tarayya da adadin Naira miliyan 117.4.
Kaduna ta biya Naira miliyan 32.06, Kogi Naira miliyan 28.6, Zamfara Naira miliyan 32.5, Delta miliyan 1.7, Kwara Naira miliyan 7, Benue Naira miliyan 16, Nasarawa Naira miliyan 55.5, Borno Naira miliyan 34.24, Neja miliyan 7, Katsina. Naira miliyan 17.5, Plateau miliyan 0.4, Adamawa Naira miliyan 9.7, Jigawa Naira miliyan 3 da Yobe N600,000.
A wani ci gaban binciken SolaceBase ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane 6847 a fadin jihohin Arewa a tsakanin watan Yuli 2023 zuwa Yuli 2024.
Zamfara ta samu mutane 1639, Kaduna 1113, Katsina 887, Borno 720, Niger 689, Sokoto 487, FCT 404, Benue 186, Kogi 170, Taraba 167, Bauchi 114, Nasarawa 113, Kwara 80, Kebbi 26, Plateau 26 , Adamawa 11, Yobe 5, Gombe 2, Jigawa 2, Kano 2.
Duk da alkawuran da gwamnati ta yi na magance matsalar rashin tsaro, bayanai sun nuna cewa har yanzu masu garkuwa da mutane na ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da tara miliyoyin nairori daga ‘yan Najeriya wadanda su ne abin ya shafa.













































