Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta kaddamar da manhajar da zatai amfani da ita wajan bawa jami’anta horo.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin ta na Twitter, tace manhajar wacce taiwa lakabi da “INEC e-school” zata maida hankali wajan bawa jami’an hukumar horo domin tunkarar babban zabe mai zuwa cikin shiri.
Hukumar tace manhajar tana da saukin fahimta wajan amfani da ita, kuma tana dauke da sautin murya da huto mai motsi, domin masu amfani da ita su fahimce yacce ake amfani da ita, ba tare da wahala ba.













































