Ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana damuwa kan hukuncin kotuna masu karo da juna, ta bukaci NJC ta dauki mataki

Kwankwaso Kwankwaso

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin karuwar yadda ake samun hukuncin shari’a masu karo da juna da kuma masu jawo cece-kuce a fadin Najeriya, inda ta yi gargadin cewa wannan yanayi na iya kawo cikas ga daidaiton dimokuradiyyar kasar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis kuma mai magana da yawunta, Dakta Habibu Sale Mohammed ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta kawo misali da sabon hukuncin da Mai shari’a Bello Kawu na babbar kotun babban birnin tarayya da ke Abuja ya yanke, a wata shari’a da ta shafi jam’iyyar NNPP, tana mai cewa wannan na daga cikin abin da ta kira yanayi mai tayar da hankali.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Laraba, babbar kotun babban birnin tarayya ta umarci INEC ta amince da kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Agbo Major, tare da watsi da bangaren ƙungiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Kwankwaso.

Ƙungiyar ta ce irin wadannan hukunce-hukuncen ba su takaita ga wuri guda ba, tana mai cewa irin wannan tsoma bakin na shari’a ya shafi harkokin cikin gida na manyan jam’iyyun siyasa, ciki har da PDP da Labour Party da ADC.

A cewar sanarwar, irin wadannan tsoma baki sau da yawa suna haifar da rudani, suna kara rikicin bangaranci, tare da raunana tsarin jam’iyyu, wanda hakan ke bude kofar yin anfani da siyasa ta hanyar da ba ta dace ba.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda kotuna masu matsayi iri daya ke yanke hukunci masu karo da juna kan lamurra iri daya, wani lokaci har suna karbar shari’o’in da suke karkashin duba na kotunan daukaka kara, inda ta yi gargadin cewa hakan na iya karya ka’idojin shari’a kamar daidaiton hukunci.

Ta kara da cewa wannan yanayi na kara haifar da tunanin jama’a cewa wasu bangarori a cikin bangaren shari’a suna shiga cikin fafatawar siyasa, wanda a cewarta na iya rage amincewar jama’a da tsarin shari’a.

Ta bayyana cewa wannan hanya mai hatsari ce ga kowace dimokuradiyya, musamman a lokacin da kasar ke shirin fuskantar muhimman zabuka.

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta bukaci jam’iyyun adawa su hada kai wajen yaki da duk wani abu da ake zargin cin zarafin bangaren shari’a ne, tare da karfafa musu gwiwa su dauki hanyoyi na doka da zaman lafiya, ciki har da wayar da kan jama’a da kare darajojin dimokuradiyya.

Ta kuma bukaci majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa NJC da ta gaggauta duba yawaitar hukunce-hukuncen da ke karo da juna tare da tabbatar da daukar mataki kan masu laifi a cikin bangaren shari’a.

Yayin da take gargadin ‘yan siyasa da su guji neman mafita ta hanyar kotuna daban-daban ko amfani da shari’a wajen cimma manufofi, ƙungiyar ta jaddada bukatar alkalai su kiyaye kwarewa da adalci da bin ka’idojin shari’a.

Ta kara da cewa bangaren shari’a dole ne ya ci gaba da zama ginshikin adalci ba tare da zama tushen rudani ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here