Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa wadanda ke da hannu a hare-haren baya-bayan nan a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, za a dauki mataki mai tsauri a kansu.
Shettima ya bayyana haka a ranar Laraba a Maiduguri lokacin da ya ziyarci wadanda suka jikkata sakamakon fashewar bam, wadanda ake jinyarsu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Mataimakin shugaban kasar ya sake jaddada kudurin gwamnatin tarayya na murkushe ta’addanci, yana mai cewa ziyarar tasa na da nufin jajanta wa wadanda suka jikkata da kuma iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa.
Ya kara da cewa baya ga umarnin da shugaban kasa ya bai wa shugabannin tsaro, gwamnatin tarayya na kara zuba jari a kayan aiki da sauran dabarun tallafi domin karfafa yaki da ta’addanci a fadin kasar.
Shettima ya yi Allah-wadai da hare-haren fashewar bam da dama da suka faru a Maiduguri a ranar Litinin, inda fiye da mutane 100 suka shafa, tare da tabbatar da mutuwar sama da mutane 20.
Ya bayyana masu aikata laifin a matsayin marasa tausayi, yana mai jaddada cewa babu wani dalili da zai halatta kashe mutane marasa laifi.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tallafa ta hanyar hukumar kula da ayyukan gaggawa ta kasa, da hukumar raya yankin arewa maso gabas, da kuma gwamnatin jihar Borno.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Shettima ya samu rakiyar mataimakin gwamnan Borno, Usman Kadafur.
Haka kuma, cikin tawagar sun hada da babbar daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, Zubaida Umar, da babban daraktan asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, Farfesa Ahmed Ahijo, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.













































