Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da biyan harajin kashi 15 cikin ɗari akan dizal da fetur da aka shigo da su.
A wasikar da aka rubuta ranar 21 ga Oktoba, 2025, sakataren musamman ga shugaban ƙasa, Damilotun Aderemi, ne ya aika da amincewar zuwa hukumar tara haraji ta cikin gida (FIRS) da kuma hukumar kula da harkokin mai da kayyade farashi ta ƙasa (NMDPRA).
Amincewar ta biyo bayan buƙatar hukumar FIRS ne domin a daidaita harajin zuwa kashi 15 cikin ɗari bisa kuɗin kaya, inshora da jigila (CIF) don daidaita farashin shigo da kaya da halin cikin gida.
Karin labari: Lauyoyi, kamfanoni, dole ne su biya kashi 7.5% na harajin VAT a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji – Gwamnatin Tarayya
Sabon tsarin zai ƙara farashin lita ɗaya na fetur da kimanin naira 99.72, bisa ƙididdigar farko da aka yi.
Biyo bayan hakan, kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ya sanar da cewa ya fara cikakken nazari kan matatun mai uku na ƙasar domin dawo da su cikin aiki.
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana hakan a shafinsa na X a daren Laraba, inda ya ce suna nazarin yiwuwar samun abokan haɗin gwiwar fasaha domin gyara ko sake tsara matatun.
Duk da kashe dala biliyan 3 wajen gyaran matatun, rahotanni sun nuna cewa sashin da ke tace ganga 60,000 na mai a rana ne kawai ya yi aiki na ɗan lokaci kafin ya tsaya, yayin da matatar Warri ke ci gaba da zama. ajiya, kuma ta Kaduna ba ta fara aiki ba kwata-kwata.













































