Ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane 10,000 daga matsugunansu a Zamfara

Ambaliya, ruwa, shafi, wasu, kananan, hukumomi, Kano, SEMA, NEMA, NiMet
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, ta ce kawo yanzu akalla kananan hukumomi uku ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a jihar. Sakataren zartarwa...

Sama da mutane 10,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da gonaki da wasu kadarori na miliyoyin Naira suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa bayan da aka shafe makonni kadan ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Sarkin Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal (mai ritaya) ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a lokacin da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya kai ziyarar tantancewa a karamar hukumar.

Lawal ya ziyarci garin Gummi da al’ummar Gayari a ranar Asabar domin duba irin barnar da ambaliyar ta yi.
Da yake zantawa da gwamnan, Mai shari’a Lawal ya bayyana yadda al’amura ke gudana a karamar hukumar.

“Bayan tattaunawar da muka yi da masana, da alama za a iya samun mafita ta dindindin. Domin tantancewar, gidaje 10,291 ne abin ya shafa amma mun fahimci cewa gwamnan zai zagaya don ganin kansa,” inji shi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here