Babban Bankin Najeriya CBN, ya ce gobarar da ta tashi a reshensa na Makurdi da safiyar ranar Alhamis an samu nasarar kasheta kuma ba ta yi barna ba.
Daraktan sashen yada labarai na Bankin, Mista Osita Nwanisobi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin babban bankib na intanet a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, “Wata karamar gobara ce ta auku a Reshenmu na Makurdi da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu na shekarar 2022, kuma cikin gaggawa aka shawo ta.
“Sakamakon daukin gaggawar da jami’an tsaro bankin suka kawo da kuma tallafin da hukumar kashe gobara ta jihar Benuwe ta bayar ya taimaka wajen kashe gobarar tare da hana yin barna a bankin.
“Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga rumbun man da ke bayan ginin bankin, wanda hakan ya sa hayaki ya turnuke ko ina.
“Yanzu haka dai an ci gaba da aiki kamar yadda aka saba a reshen bankin,” in ji Nwanisobi.













































