Kotu ta saka ranar gurfanar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da matarsa ​​da wasu mutum 6

Ganduje, kotu, gurfanar, ranar, tsohon, gwamnan, kano, gwamnati
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai gurfana a gaban wata babbar kotun Kano ranar 17 ga watan...

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai gurfana a gaban wata babbar kotun Kano ranar 17 ga watan Afrilun 2024.

A cikin sammacin da jaridar SOLACEBASE ta gani, a ranar Talata, Abdullahi Umar Ganduje zai gurfana a gaban kotu tare da matarsa, Hafsat Gaduje da wasu mutane shida bisa laifuka takwas da suka hada da cin hancin dala da karkatar da wasu kudade da suka hada da Dala 413,000 da cin hancin Naira Biliyan 1.38 da sauransu.

Karin labari: Fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso ta rasu tana da shekara 56

SOLACEBASE ta rawaito cewa sauran wadanda ake karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje da Hafsat Umar da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da kuma Jibrilla Muhammad sai Lamash Properties Ltd da Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

Gwamnatin jihar Kano da ta shigar da kara a gaban kotu ta ce ta tattara shaidu 15.

Karin labari: Gwamnan Kano ya sake nada Imam Ogan Boye mukaminsa

Batun da aka sanya ranar 17 ga watan Afrilun 2024 yana gaban mai shari’a Usman Malam Na’aba na babbar kotun jiha mai lamba hudu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here