’Yan Majalisa 27 Sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC A Ribas

Rivers Assembly members new 750x430
Rivers Assembly members new 750x430

Siyasa a Jihar Ribas ta dauki sabon salo inda 27 daga cikin ’yan majalisar dokokin jihar 32 suka sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Enemi George, ya tabbatar da hakan ga manema labarai cewa yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule.

Ya ce sun dauki matakin ne a zaman da suka yi da safiyar ranar Litinin.

An shafe makonni ana takun saka tsakanin Amaewhule da wani dan majalisa mai suna Edison Ehie kan rikicin shugabancin majalisar.

Ana kyautata zaton Amaewhule na yin biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike yayin da shi kuma Ehie yake na hannun dama Gwamna Siminalayi Fubara ne.

Majalisar a karkashin Amaewhule a watan Oktoba ta gabatar da sanarwar tsige gwamnan tare da tsige Ehie a matsayin shugaban majalisar.

Sai dai nan take wasu ’yan majalisar masu biyayya ga Fubara suka tsige Amaewhule tare da nada Ehie a matsayin sabon shugaban majalisar.

Rikicin da ya barke a majalisar mai mambobi 32 ya samo asali ne daga rashin jituwar Fubara da uban gidansa, Wike, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya.

Duk da cewa ’yan siyasar biyu sun halarci taro makonnin da suka gabata kuma ga dukkan alamu an samu sasanci.

Amma da ficewar ’yan majalisar 27 daga  PDP zuwa APC a ranar Litinin ya bude sabon babi a siyasar jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here