A buga sunayen wadanda aka kashe, sannan a biya iyalansu diyya-Jam’iyyar LP

Tudun Biri attack 720x430 (1)
Tudun Biri attack 720x430 (1)

Mako guda bayan tashin bam a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta Labour ta bukaci a biya iyalan wadanda suka mutu diyya, sannan ta buga sunayen wadanda aka kashe a harin.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Obiora Ifoh, ya fitar a ranar Lahadi ya yi gargadin cewa tayar da bam din ba abu ne da za a ce kuskure ba.

Idan za a iya tunawa dai harin bam din da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama ya sha Allah wadai da tilasta mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ziyartar iyalan wadanda suka mutu.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Karanta wannan:Hukumar NDLEA ta tarwatsa gasar shan kwayoyi a gidan biki tare da kama Ango  

A ranar Lahadin nan ne majalisar dattawan ta bi sahun takwarorinsu na arewa domin bayar da gudummawar albashin watan Disamba ga wanda abin ya shafa a ziyarar jaje da suka kai jihar.

Duk da wannan tashin bam din mara dadi, jam’iyyar Labour ta jaddada cewa “tana matukar alfahari da sojojin Najeriya,” saboda “sun nuna kwazo a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here