ASUU ta bukaci shugaba Buhari ya gana da kwamitin Briggs kafin ta janye yajin aikin da ta keyi

ASUU leader 1
ASUU leader 1
Kungiyar malaman jami’o’i,  ta kasa ASUU, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gana da kwamitin sasanta wa da Farfesa Nimi Briggs ke jagoranta.

Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osekede ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN jiya Talata a Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta kafa Kwamitin Briggs a ranar 7 ga watan Yuni, domin ya sake tattaunawa da kungiyar ASUU a kan yarjejeniyar 2009 tare da mika rahotonsa ga ministan ilimi, Adamu Adamu cikin watanni uku.

Buhari , a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce “ajiye dalibai a gida ya isa haka.”

Sai dai kuma Osedeke ya ce: “Ban fahimci dalilin da ya sa shugaban kasar ya ce “ya isa ba”, alhali ba mu ne mu ka janyo daliban ke ci gaba da zaman daɓaro a gida ba.

“Gwamnatin tarayya ta aiko da tawagarta domin tattaunawa da mu kuma mun gama. Maimakon ta dawo wurinmu ta faɗa mana sakamakon tattaunawar, sai kuma mu ke jin haka.

Ya bukaci Buhari da ya gana da kwamitin tattaunawa da kuma sanya hannu kan rahoton.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here