Buhari zai tafi Landan bikin naɗin sarkin Birtaniya

Buhari departs
Buhari departs

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je Landan domin halartar bikin naɗin sabon sarkin Birtaniya Charles lll.

A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari zai bar Najeriya ranar Laraba 3 ga watan Mayu, don halartar bikin naɗin sarki Charles lll.

Za a gudanar da bikin naɗin ne ranar Asabar 6 ga watan Mayu a fadar sarkin da ke Birtaniya.

Sanarwar ta ce gabanin bikin naɗin sarautar, ƙungiyar ƙasashe renon Ingila ta Commonwealth za su gudanar da taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ranar Juma’a 5 ga watan Mayu.

Yayin wannan bulaguron shugaba Buhari zai samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da ministan harkokin ƙasashen waje Geoffrey Onyeama, da ministan yaɗa labarai Lai Mohammed.

Sauran su ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da Daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar, da wasu manyan jami’an gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here