Wata matashiya mai suna Lawal Hameedat Adenike ta kai karar hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da PEFTI a gaban kotu bisa zargin su da tilasta mata cire hijabi kafin ta rubuta jarabawar (UTME).
Mahaifiyarta da lauyanta ne suka shigar da karar a madadinta.
Da take magana da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Basirat Ojo, mahaifiyar Lawal Hameedat ta ba da labarin abin da ya faru a ranar 25 ga Afrilu, 2025 a Cibiyar CBT ta PEFTI da ke Ibadan, Jihar Oyo.
Ta bayyana cewa, “An gaya wa ‘yata cewa ba za ta iya rubuta jarabawar ba, sai dai idan ta cire hijabin da take sakawa saboda addini, wannan abu ne mai raɗaɗi da wulakanci a gare ta, a matsayina na mahaifiyarta, sai na ɗauki mataki don kare haƙƙinta.
Karin karatu: Hajj 2025: Ku kiyaye mutunci da martabar Najeriya a Saudiyya – Shettima ya fadawa maniyyata
Shari’ar dai ta bukaci hukumar JAMB da PEFTI su nemi afuwar jama’a, ta hanyar buga su a jaridun kasar guda biyu, tare da biyan ta diyya saboda tauye mata hakkinta.
Haka kuma tana neman kotu ta bayyana duk wata doka da ta bukaci dalibai mata su cire hijabi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Karanta: JAMB ta fitar da sakamakon UTME ta shekarar 2025
Qousim Opakunle, lauyan Lawal Hameedat, ya jaddada tushen shari’ar.
Ya ce, “Wannan bukatar ta ci karo da sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya tabbatar da ‘yancin tunani, da kuma addini, hakkinmu ne mu kare wadannan muhimman hakkokin, musamman ga kananan yara wadanda ba za su iya kare kansu ba.”