Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wasu tankokin mai guda biyu suka fashe a gidan man MRS da ke kusa da filin jirgin sama na Yola a jihar Adamawa.
Fashewar kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, ta faru ne a lokacin da wata tankar mai take sauke man da ta dauko.
Karanta har ila yau: Gobara ta lalata ofishin Rediyon Najeriya da ke Legas
“Mun ji karar kara mai karfi kuma tashar mai ta tashi da wuta yayin da wata tankar mai ke saukewa,” wani dan kasuwa da ke kusa da wajen ya bayyana lamarin.
Fashewar ta haifar da gagarumar tashin wuta wadda ta mamaye tashar da kuma yankunan da ke kusa.
A halin da ake ciki dai jami’an kashe gobara ta jihar Adamawa, da hukumar kashe gobara ta tarayya, na ci gaba da kokarin shawo kan gobarar.