Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci zaman lafiya da hakuri a tsakanin mazauna garin Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo, biyo bayan rikicin fili da ya barke tsakanin al’umma da jami’ar Bayero Kano (BUK).
Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji.
Labari mai alaƙa: Jami’an tsaro sun kewayw gidan Sarkin Kano Sanusi tare da hana shige da fice
Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikansu, wadanda suka jikkata Allah ya ba su lafiya cikin gaggawa.
“Dole ne mu yi addu’a ga rayukan wadanda suka mutu da kuma baiwa iyalansu karfin jure wannan rashi, muna fatan wannan ya zama na karshe daga cikin irin wadannan abubuwa masu ban tausayi da za su faru a cikin al’ummarmu,”.
SolaceBase ta ruwaito cewa Sarkin ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu kamun kai tare da bi hanyoyin da suka dace don gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa tashin hankali yana haifar da karin wahala ne kawai.













































