Jami’an tsaro sun kewayw gidan Sarkin Kano Sanusi tare da hana shige da fice

1733477673301

A yau safiyar Juma’a an tashi da ganin jami’an ƴansanda ɗauke da makamai tare da na SSS sun yi ƙawanya a Masarautar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi ll ke zaune.

Solacebase ta tattaro cewa jami’an tsaron sun hana shige da fice a gidan Sarkin.

Rahotanni sun baiyana cewa a yau din ake sa ran Sarki Sanusi zai raka sabon Wamban Kano, Munir Sanusi zuwa Bichi, inda zai yi hamkimci.

Solacebase ta jiyo cewa can ma fadar harkokin na Bichi an zuba jami’an tsaro, mai yiwuwa da nufin hana zuwan sabon Wamban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here