Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya dage dokar toshe layukan sadarwar wayar salula a jihar.
Matawalle ya bayyana hakan ne a babban taron jam’iyyar APC na jihar a Gusau ranar Asabar.
Matawalle ya ce Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta saki dukkan hanyoyin sadarwa zuwa ranar Litinin.
Ya ce gwamnatinsa ta gamsu da yanayin tsaro a jihar.
Matawalle ya ce an dakile ayyukan ‘yan fashi da garkuwa da mutane a tsawon lokacin da aka rufe layin sadarwa.
Gwamnan ya kara da cewa har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da kwararowa tare da kame ragowar ‘yan bindigar da sauran abokan huldar su.
Matawalle ya ce “An yanke shawarar ne saboda karfafa rahotannin nasarorin da aka samu a jihar daga wadannan tsauraran matakan.”
Idan za a iya tunawa a ranar 4 ga watan Satumba ne hukumar NCC ta dakatar da harkokin sadarwa a jihar domin toshe hanyoyin sadarwa tsakanin ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da kuma abokan huldar su a jihar.
Hukumar ta NCC, ta dage dakatarwar tare da dawo da ayyukan sadarwar a Gusau, babban birnin Zamfara a ranar 4 ga watan Oktoba yayin da kananan hukumomi 13 suka rage ba tare da hanyar sadarwar ba.
Matawalle ya yabawa mazauna yankin bisa jajircewa da hakurin da suka yi na tsawon watanni uku na dakatarwar da aka yi a cibiyar sadarwa.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su koma jam’iyyar APC, inda ya kara da cewa maido da sadarwar zai taimaka wa jam’iyyar wajen yin rajistar shiga jam’iyyar.













































