Abdul Aliyu, Manjo Janar mai ritaya kuma Tsohon Shugaban Tsaro na Musamman na Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Kasa ya yi watsi da matsin lambar da wasu jami’an soji suka yi masa na tsawaita shirin sauya mulki da ranar mika mulki bayan ya karbi mulki a shekarar 1998.
Aliyu ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar yayin bikin cikar Abdulsalami shekaru 84 da kuma kaddamar da sabbin littattafansa 3, ciki har da littafin tarihin rayuwarsa.
Da yake jawabi a matsayin shugaban kwamitin shirya bikin cika shekaru 84 na tsohon Shugaban Kasar, Aliyu ya bayyana Abdulsalami a matsayin shugaba da ya kasance cikin shirin yanke shawarwari masu wuya domin muradan kasa, har ma da wadanda suka saba da muradin manyan jami’an soji masu tasiri.
Ya ce bayan Abdulsalami ya sanar da shirin mika mulki na watanni 6 bayan ya zama shugaban kasa a 1998, ra’ayoyi a tsakanin sojoji sun rabu sosai.
A cewar sa, yayin da wasu jami’ai suka goyi bayan lokacin da aka saka, wasu kuma sun so a tsawaita shi, inda suka bada hujjar cewa farar hula ba su shirya karbar mulki ba.
“Lokacin da ya fitar da shirin sauya mulki na watanni 6, jami’an soji sun kasu kashi 3,” in ji Aliyu.
“Kashi daya sun yi imanin cewa, eh, wannan shi ne abin da ya dace a yi.
“Kashi na biyu sun ce hakan ya yi, amma ya kamata a tsawaita shi da watanni 5 zuwa 6.
“Kashi na uku sun yi imanin cewa farar hula ba su shirya karbar kasar ba.”
Aliyu ya ce ya tuntubi Abdulsalami da damuwar da jami’an da suka goyi bayan tsawaita sauya mulkin suke yi.
“Na je wurinsa na ce, ‘Ranka ya dade akwai wadanda ke tambaya ko za mu iya tsawaita watanni 6 domin mu jawo ra’ayin wadannan mutane zuwa bangarenmu’,” in ji shi.
“Ya kalle ni ya ce, ‘Aiki na ne da nauyi na in yanke shawara a madadin kasa da kuma abin da ya zai yi kyau ga kasa da mutane, na yanke shawarata wannan zan yi.’”
Aliyu ya ce wannan amsar ta nuna jajircewar Abdulsalami wajen mayar da Najeriya kan tsarin mulkin demokuradiyya duk da matsin da ya fuskanta daga ko’ina.
“Ya kasance cikin shirin yin komai, har ma da yin adawa da kansa, domin tabbatar da an yi abin da ya dace ga kasa,” in ji shi.
Abdulsalami ya zama shugaban kasa a watan Yuni 1998 bayan rasuwar Sani Abacha.
Ya jagoranci shirin sauya mulki wanda ya kai ga rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kasa da aka zaba ta hanyar demokuradiyya a ranar 29 ga Mayu 1999, lamarin da ya kawo karshen shekaru da dama na mulkin soji.













































