Hedikwatar tsaro ta ce zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan na da nufin maimaita abin da ya faru a Kenya ne.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya ce bisa la’akari da bayanan sirri da suke da shi, wasu marasa gaskiya za su yi awon gaba da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.
Buba ya ce, “Manufar zanga-zangar ita ce a nuna muku abubuwan da ke faruwa a kasar Kenya. Kuma zan kara da cewa abin da ke faruwa a Kenya dangane da zanga-zangar, na daya shi ne tashin hankali. Na biyu ya kasance ba’a warware shi ba yayin da muke magana yanzu.
Karin labari: Mutane 3 sun rasu a ruftawar wani gini a Legas
A cewarsa, sojoji a shirye suke akai idan lamarin ya sha kan ‘yan sanda, ya kuma yi gargadin cewa ba za’a amince da wani yanayi na rashin zaman lafiya ba kamar yadda aka yi niyya na zanga-zangar lumana domin na iya kawo rudani a kasar.
“Dangane da abin da aka tattara, akwai shirin da wasu marasa kishin kasa ke yi na wannan zanga-zangar da kuma tabbatar da cewa ta rikide zuwa tashin hankali, ina ankarar da ku abinda muke hange a gaba ne kamar yadda zai iya faruwa.”