Hukumar NDLEA ta cafke mutum 22 masu safarar kwayoyi a Kano

NDLEA, Hukumar, cafke, mutum, masu, safarar, kwayoyi, Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta samu nasarar kama wasu dillalan kwayoyi 22 a jihar a watan Yulin 2024...

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta samu nasarar kama wasu dillalan kwayoyi 22 a jihar a watan Yulin 2024.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a Kano, Abubakar Idris-Ahmad ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Kano.

Ya ce hukuncin babbar nasara ce a yaki da safarar miyagun kwayoyi da hukumar ta yi.

“Daga cikin dillalan miyagun kwayoyi 22 da aka yankewa hukuncin, wani Abubakar Mu’azu da aka kama ya fuskanci mummunar hatsaniya wadda ta ga jami’in NDLEA ya caka masa wuka.

Karin labari: Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu shirin yin zanga-zanga

“An gurfanar da Mu’azu a gaban kotu kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali, yayin da sauran wadanda aka yankewa ukuncin zaman gidan yari daban-daban.

“An samu wasu haramtattun abubuwa a hannunsa,” in ji Idris-Ahmad.

Kwamandan ta’ammali da miyagun kwayoyi ya ce rundunar za ta ci gaba da yaki da safarar miyagun kwayoyi tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Idris-Ahmad ya yabawa shugaba kuma babban jami’in hukumar, Burgediya-Janar. Mohammed Buba-Marwa, saboda goyon baya da jajircewarsa wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Karin labari: Hukumar NDLEA ta kama wani mutum da ake nema ruwa a jallo

Ya ce babu wani abin tsoro ko tashin hankali da zai hana jami’an hukumar bin diddigi tare da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.

“Jami’an mu kwararru ne masu horarwa wadanda ba za su daina komai ba don tabbatar da cewa wadanda ke aikata laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi sun fuskanci fushin doka,” inji Idris-Ahmad.

Ya nemi goyon bayan jama’a tare da bukatar su kasance masu taka-tsan-tsan da kai rahoton duk wani abu da ake zargi da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi ga hukumar kamar yadda NAN ta tabbatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here