Gwamnonin Arewa na taro kan matsalar tsaro a Kaduna

a091dccb 1e3a 4203 bbd5 fa00a6c61911.jpg (2)

Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.

Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin.

Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waɗanda ke halartar taron.

Karanta: Gwamna Zulum ya sake tsugunar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu

A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here