Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta soke taron da ta shirya gudanarwa a jihar Kano.
Sakataren kwamitin yakin neman zaben, James Faleke a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ya ce an soke taron da aka shirya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu.
Mista Faleke bai bayar da wani dalili na soke taron ba.
Gangamin farko dai ya gudana ne a ranar 4 ga watan Janairu a Kano a filin wasa na Sani Abacha amma bisa jadawalin jam’iyyar ta tsara aiwatar da karbar bakuncin jam’iyyar har sau biyu.
Sai dai babu tabbaci ko soke taron na da alaka da korafe korafen da ake yi kan karancin Naira a fadin kasar.










































