Shugaban kasa Buhari ya kafa kwamitocin koli na mika mulki

BUHARI signs signs 750x430 1
BUHARI signs signs 750x430 1

Rahotanni sun ce ayau Alhamis shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mika mulki a shekarar 2023.

Buhari ya kuma rattaba hannu kan dokar zartarwa mai lamba 14 na shekarar 2023 kan saukakawa da gudanar da sauye sauyen shugaban kasa.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Willie Bassey ya fitar a ranar Alhamis ta tabbatar da faruwar lamarin.

“ Sakataren gwamnatin tarayya ne zai kaddamar da majalisar mika mulki a ranar Talata 14 ga Fabrairu, 2023 da karfe 12 na rana a dakin taro na SGF, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya ce ana sa ran mambobin za su halarci bikin kaddamar da su kai tsaye.

‘’Babban abin da ke cikin dokar zartarwar shugaban kasa mai lamba 14 na shekarar 2023 ita ce kafa tsarin shari’a da zai ba da damar mika mulki ba tare da wata matsala ba daga wannan gwamnatin ta shugaban kasa zuwa waccan wani bangare na gadon shugaba Buhari.

Mambobin kwamitin sune:

Sakataren Gwamnatin Tarayya – Shugaba

Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya

iii. Babban Lauyan Tarayya kuma Babban Sakatare, Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya

Sakatarorin dindindin daga ma’aikatu da ofisoshin Kudi, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, maaikatar harkokin Waje, labarai da Al’adu

Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA)

Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati

Ofishin Harkokin Majalisar, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Ofishin Babban Ayyuka, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Ofishin Harkokin Tattalin Arziki da Siyasa, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Mai Ba shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro

Babban Hafsan Tsaro

vii. Sufeto-Janar na ‘yan sanda

viii. Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa

Darakta Janar, Hukumar Tsaro ta Jiha

Babban magatakardar kotun kolin Najeriya; kuma

Wakilai guda biyu, wanda zababben shugaban kasa zai nada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here