Najeriya ta ki amincewa da kudirin sake fasalin sashin zaman lafiya da tsaro na AU

Nigeria ready to play vital role in G20 Tinubu 720x430

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da kudirin samar da wani sabon sashe daga sashin kula da harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka (AU).

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ta goyi bayan yunkurin yin garambawul ga kungiyar tarayyar Afirka, wanda hakan ya sanya kungiyar ta kasance mai fa’ida, mai inganci, da kuma dacewa da bukatun kasashe mambobinta, ta fuskar sauyin yanayi na siyasa da tattalin arziki a duniya cikin hanzari.

Shugaba Bola Tinubu, wanda ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya gabatar da jawabinsa a yayin nazari da tattaunawa kan rahoton sake fasalin kungiyar ta AU, ya yabawa takwarorinsa na Rwanda da Kenya, Paul Kagame da Williams Ruto, bisa shawarwarin yin garambawul din.

Karin karatu: Shugaba Tinubu ya yi kira a samar da cibiyar yaki da ta’addanci a Afrika

Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi ya amince da shawarwarin da aka zayyana a cikin daftarin kudurin na sake fasalin kungiyar ta AU, ya kuma ce gwamnatin Najeriya na goyon bayan shawarar kafa kwamitin sa ido kan shugabannin kasashe da gwamnatoci kan sauye-sauyen kungiyar AU karkashin jagorancin shugaba Ruto.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma amince da kudirin na cewa jadawalin taron kolin kungiyar ta AU bai wuce wasu muhimman abubuwa guda uku ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here