Gwamnatin jihar Kano ta yi kakkausar suka ga shirin jam’iyyar APC na kafa gwamnatin bibiya, inda ta bayyana yunkurin a matsayin wanda ya sabawa ka’ida, da rashin bin tsarin mulkin kasa, da kuma neman durkusar da siyasa.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a ranar Lahadi, ya soki matakin da Alhaji Usman Alhaji, shugaban kungiyar yan balantiyar kishin kasa a jam’iyyar APC ta kasa ya sanar, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da babbar illa a shari’a da zamantakewa.
“Bari in tunatar da wadannan jiga-jigan jam’iyyar APC na Kano cewa, a tsarin dimokuradiyya irin namu, kafa gwamnati a cikin gwamnati kwata-kwata haramun ne kuma ba bisa ka’ida ba,” in ji Waiya.
“Gwamnatin bibiya, kamar yadda ake yi a Burtaniya, tana wanzuwa a cikin tsarin majalisar dokoki inda jam’iyyun adawa ke nada ‘ministan bibiya’ don tantance gwamnatin da ke mulki.
Ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo rudani a jihar ba, domin yin hakan makirci ne APC ke shirya wa.