Makonni guda bayan tallafa wa dalibai 70 don karatun digiri na biyu a kasashen waje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, zai ba da tallafin karatu ga dalibai 300 domin yin digiri na biyu a jami’o’in Najeriya.
A wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan kafafen watsa labarai, Ismail Mudashir, an bayyana cewa asusun tallafinsa (Barau I. Jibrin Foundation) ya buɗe neman tallafin digiri na biyu na cikin gida don shekarar karatu ta 2025/2026.
Shirin zai ba da dama ga karatun kimiyya da fasaha a fannoni daban-daban kamar Artificial Intelligence, Cyber Security, Oil and Gas Operations, Climate Change Management, da Mechatronics.
Jami’o’in da aka zaɓa sun haɗa da Jami’ar Bayero Kano, ABU Zaria, Jami’ar Ibadan, da OAU Ile-Ife. Wannan yunkuri na nufin habaka ilimi da ƙwarewar matasa don ci gaban ƙasa.