Gwamnan Jihar Delta Oborevwori ya dakatar da Omoun Perez

Gwamnan, Jihar, Delta, Oborevwori, dakatar,
Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya bayar da umarnin dakatar da kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Omoun Perez ba tare da bata lokaci ba...

Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya bayar da umarnin dakatar da kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Omoun Perez ba tare da bata lokaci ba.

Hakazalika, gwamnan ya umarci babban sakatare na ma’aikatar, Bennett Agamah mataimakin Darakta da Injiniyan Aikin Noma Oki Yintareke da kuma Babban Akanta Gabriel Idiatacheko, “ci gaba da hutun dole har sai an samu sanarwa bisa ka’idojin ma’aikatan gwamnati.”

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fintiri a matsayin Gwamnan Adamawa

Wata sanarwa da ta tabbatar da matakin na dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dakta Kingsley Emu, kuma ta mika wa manema labarai ranar Laraba a garin Warri na jihar Delta.

Sanarwar ta bayyana cewa matakan sun zama wajibi, “bayan sakamakon bitar aiwatar da aikin Greenhouse da Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa ta Jiha ta yi.”

Ya kara da cewa an dauki matakin ne “saboda rahoton wucin gadi na kwamitin da kuma samun damar samun bayanai ba tare da wata matsala ba a lokacin binciken.”

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da kwamitin Ma’aikata 37 na mafi karancin albashi

An bayyana cewa, “Oborevwori ya kafa wani kwamiti mai mutum bakwai karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Dr. Kingsley Emu don bincikar da’awar da kuma yadda aka samu sabani da suka shafi gudanar da shirin na ma’aikatar.

“Ayyukan da gwamnati ta yi ba wai zato na laifi ba ne, sai dai matakin da ya dace don tabbatar da tsarin binciken da aka riga aka kafa wanda shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken ba tare da nuna son kai ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here