Gwamna Adeleke ya sanya dokar hana fita bayan mutuwar mutum 2 a rikicin Jihar Osun

Gwamna, Adeleke, Osun, dokar, hana fita, jihar
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya sake sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe a yankin Ilobu da Ifon, biyo bayan sabon rikicin...

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya sake sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe a yankin Ilobu da Ifon, biyo bayan sabon rikicin da ya sake barkewa a garuruwan.

Adeleke ya kuma tara rundunar hadin gwiwa tare da tura jami’an tsaro ciki har da na soji zuwa yankunan da ke rikicin.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a Kolapo Alimi ya fitar a ranar Talata ya sanar da matakin da gwamnan ya dauka.

Karanta wannan: Gwamnan Jihar Delta Oborevwori ya dakatar da Omoun Perez

Idan dai za a iya tunawa, a ranar litinin ne mayakan sa kai na al’ummar Ilobu da Ifon suka sake fafatawa a kauyukan da ke kan iyakar jihohin Osun da Oyo.

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 tare da lalata dukiyoyi a rikicin da ya barke.

Kafin rikicin na baya-bayan nan, a watan Oktoban shekarar da ta gabata Adeleke ya sanya dokar ta-baci a tsakanin al’ummomin biyu bayan barkewar kazamin fadan da ya barke.

Sai dai an dage dokar hana fita a watan Disamba bayan dawowar zaman lafiya a yankin.

Sai dai a ranar litinin ne rikici ya sake barkewa, lamarin da ya sa mazauna garin da dama suka tsere.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fintiri a matsayin Gwamnan Adamawa

Sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Talata, ta ce,  “Da yake nazari kan lamarin tsaro, mai girma Sanata Ademola Adeleke, a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar, ya amince da kafa dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe nan da nan.

“Ya kamata gwamnatin jihar Osun ta kafa rundunar hadin gwiwa ta dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al’ummomin da ke fada da juna, wadanda za su hada da sarakunan gargajiya na Ifon da Ilobu da Erin na Osun nan take.

“Za a gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki tare da dukkan sarakunan gargajiya da sarakunan al’ummomin uku tare da jami’an gwamnati da dukkan shugabannin tsaro. Cewa a tura tawagar dukkan jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, da Civil Defence zuwa ga al’ummomin da ke fada cikin gaggawa.”

Karanta wannan: ‘Yan ta’adda sun kashe mutane 30 tare da kone kauyuka 2 a Mali

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Osun ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a rikicin kabilanci tsakanin Ifon da Ilobu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Yemisi Opalola ta fitar, yayin da take kira da a kwantar da hankula, ta ce an tura jami’an tsaro a yankin domin dawo da zaman lafiya.

“Abin takaici mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon lamarin, kuma an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa da ke jihar.

“A halin da ake ciki wani Mojeed Oyewumi Alani da wani daya da jami’an ‘yan sanda suka kama da makamai da laya saboda rawar da suka taka a rikicin kabilanci an mika su zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi,” in ji Opalola.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here