‘Yan ta’adda sun kashe mutane 30 tare da kone kauyuka 2 a Mali

mali, 'yan ta'adda,

Mahukuntan Mali sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 30 yayin wasu mabanbantan hare-hare biyu da ‘yan ta’adda suka kai kan kauyukan tsakiyar kasar a ranakun karshen makon da ya gabata.

Magajin garin yankin Bankass Moulaye Guindo da ke tabbatar da faruwar hare-haren ga manema labarai yayin wata hirarsa da wata kafa ta wayar tarho, ya ce ‘yan ta’addan sun farmakin kauyukan Ogota da Oimbe da ke kewayen Bankass a yankin Mopti.

Duk da cewa magajin garin bai bayyana hakikanin kungiyar da ke da hannu a harin ba, amma Mali na fama da hare-hare ne daga kungiyoyin da ke biyayya ga al Qaeda wadanda ke ikirarin jihadi da karfin tsiya.

Karanta wannan: Najeriya ta samu rangwame 5 na matsayin cin hanci da rashawa – TI

A cewar magajin garin na Bankass ‘yan ta’addan sun rufarwa kauyukan biyu da harbi kan mai uwa da wabi baya ga kone ilahirin gidajen da suka ci karo da su.

Guindo ya shaidawa Reuters cewa ‘yan ta’addan sun kashe jumullar mutum 30 da suka kunshi maza da mata da yara kanana yayinda suka jikkata wasu da dama.

Karanta wannan: Kasashen Mali da Burkina Faso sun mikawa ECOWAS wasikar ficewa a hukumance

Ko a jiya Litinin sai da ‘yan ta’addan suka kai makamancin harin a kauyen Dialassagou ko da ya ke babu cikakken bayanin irin barnar da suka yi.

Mali wadda ta shafe fiye da shekaru 10 ta na fama da matsalolin ‘yan ta’adda da ya kai ga juyin mulkin Soji har sau 2 a shekarar 2020 da 2021, yanzu haka ta na karfafa alakarta da Rasha ne a kokarin magance matsalolin tsaron musamman bayan raga gari da Faransa wadda ta yi mata mulkin mallaka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here