Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa matsalolin da suka daɗe suna tattare da rikicin masarautar Kano za su samu mafita cikin lumana nan ba da jimawa ba, domin dawo da kwanciyar hankali da zaman lafiya a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin magance rikicin da ya shafi masarautar.
Gwamnatin ta tuna cewa Muhammadu Sanusi na biyu an naɗa shi a matsayin sarkin Kano na goma sha shida a watan Mayun shekarar 2024, bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Aminu Ado Bayero daga sarautar.
Wannan mataki ya biyo bayan sanya hannu kan dokar soke majalisar masarautun jihar Kano ta shekarar 2024, wadda ta maye gurbin dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 tare da rusa masarautun da gwamnatin da ta gabata ta kafa.
Ibrahim Waiya ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa an riga an tanadi matakan dawo da zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali a faɗin jihar, yana mai cewa gwamnatin jihar na da cikakken shiri na tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano tana tafiya ne bisa bin doka da oda, girmama al’adun gargajiya, tare da la’akari da muradun jama’ar Kano gaba ɗaya, domin kauce wa ci gaba da tashin hankali ko barazana ga tafiyar da mulki.
Dangane da sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC, kwamishinan ya bayyana cewa wannan mataki zai haifar da fa’ida mai yawa ga jihar Kano, musamman ta fuskar kusanci da gwamnatin tarayya da kuma samun ƙarin ayyuka da tsare-tsaren ci gaba.
Ya ƙara da cewa jama’ar Kano za su ci gaba da cin ribar dimokiraɗiyya ta hanyar ƙarin tallafi, ayyukan raya ƙasa, da tsare-tsaren ci gaba a fannoni irin su ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da walwalar al’umma.
NAN












































